Sojojin Nijer Sun Kashe Manoma 14
Dakarun gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun kashe wasu fararen hula a wani farmakin da suka ce na kuskure a yankin Abadam na jihar Diffa da ke kan iyakar kasar da Najeriya.
Rahotanni dake fitowa daga jumhoriyar niger na cewa Sojojin kasar sun kashe wasu fararen hula 14 a wani farmakin kuskure da suke zaton mayakan Boko Haram ne, a yankin Abadam da ke kan iyakar kasar da Najeriya.
Wani babban jami'i a yankin, ya ce sojojin gwamnatin Nijar din na sintiri ne a wuraren da aka haramtawa mutane gittawa a yankin na Abadam cikin yankin Diffa, inda suka buda wuta kan talakwan, da aka gano cewa wasu manoma ne.
Biyu daga cikin wadanda sojin suka kashe 'yan kasar Nijar ne, sauran 12 kuwa bayanan mahukunta sun ce 'yan Najeriya ne. Lamarin dai na faruwa ne kwanaki uku da mayakan Boko Haram suka kashe mutane tara tare da yin awan gaba da wasu masu yawa.