Nijar : 'Yan Ci-Rani Masu Yawa Sun Tsallake Rijiya Da Baya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22006-nijar_'yan_ci_rani_masu_yawa_sun_tsallake_rijiya_da_baya
Jami'an tsaron kasar Nijar sun ceto da 'yan gudun hijira masu yawa daga mutuwa a cikin saharar arewa maso gabacin kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 08, 2017 06:52 UTC
  • Nijar : 'Yan Ci-Rani Masu Yawa Sun Tsallake Rijiya Da Baya

Jami'an tsaron kasar Nijar sun ceto da 'yan gudun hijira masu yawa daga mutuwa a cikin saharar arewa maso gabacin kasar.

Jami'an tsaron kasar Nijar sun ceto da 'yan gudun hijira masu yawa daga mutuwa a cikin saharar arewa maso gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto majiyar jamhuriyar Nijar a jiya juma'a cewa; " A ranar larabar da ta gabata,  jami'an tsaron kasar sun ceto da 'yan ci-ranin 67 da su ka fito daga cikin kasashen yammacin Afirka, a cikin saharar Séguédine.

Majiyar ta ci gaba da cewa mutum guda daga cikin 'yan gudun hijirar ya rasa ransa saboda yanayi mai wahala da ya shiga.

Samarin nahiyar Afirka na kokarin isa kasashen turai ta bin hanyoyin masu hatsari da a wasu lokuta su ke rasa rayukansu.