Unicef Ta Nada Alfaga Na Nijer Jakadanta Na Musamman
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22016-unicef_ta_nada_alfaga_na_nijer_jakadanta_na_musamman
Asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF ya nada Abdoulrazak Issoufou Alfaga, zakaran duniya na wasan kokowar Taekwando dan kasar Nijar a matsayin jekadansa na musamman.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 08, 2017 11:56 UTC
  • Unicef Ta Nada Alfaga Na Nijer Jakadanta Na Musamman

Asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF ya nada Abdoulrazak Issoufou Alfaga, zakaran duniya na wasan kokowar Taekwando dan kasar Nijar a matsayin jekadansa na musamman.

Alfaga ya kasance mutum na farko a Nijar da ya zama jekadan UNICEF, kuma en ce zai shafe shekaru biyu yana aiki da hukumar.

A makon da ya gabata ne Alfaga ya lashe gasar wasan kokowar Taekwando ta duniya da aka gudanar a Koriya ta kudu.

Dan wasan ya samu kyakkawar tarba daga Al'ummar kasar bayan ya isa  kasar ta Nijar inda Shugaba  Mahamadou Issoufou da kansa  ya karrama shi da lambar yabo mafi girma a kasar.