Nijar : An Cafke Mutane Da Dama, Bisa Laifin Kashe Dorina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22020-nijar_an_cafke_mutane_da_dama_bisa_laifin_kashe_dorina
Hukumomi a yankin Ayoru dake yammacin jamhuriya Nijar sun sanar da cafke gomman mutane bisa laifin kashe wata dorina ba bisa ka'ida ba.
(last modified 2018-08-22T11:30:21+00:00 )
Jul 08, 2017 14:56 UTC
  • Nijar : An Cafke Mutane Da Dama, Bisa Laifin Kashe Dorina

Hukumomi a yankin Ayoru dake yammacin jamhuriya Nijar sun sanar da cafke gomman mutane bisa laifin kashe wata dorina ba bisa ka'ida ba.

Dorina dai na daga cikin jerin jinsin namun dajin dake karkashin kula saboda barazanar bacewarsu a doron kasa.

Wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunnansa ba ya shaidawa gidan radiyon Kalangu cewa dorinar ta farmawa wani sa ne, lamarin da ya sa mazauna kauyen suka dauki mataki a kanta.

Kantoman yankin na Ayoru, Jamdo Richi Ag Alher ya tabbatar da cafke mutanen.

Mutanen yankin dai sun jima suna korafi kan yawaitar barnar da dorina ke yi masu a cikin gonnaki da kuma hallaka masu dabbobi, inda suka bukaci hukumomi dasu samarwa da namun dajin na dorina wani wurin kiwo na daban.

A shekara 2014 daliban makaranta 12 ne suka rasa rayukansu a wani hari da wata dorina ta kai ma kwale-kwalen da suke ciki a kogin Niger, daga bisani dai hukumin kasar suka sa aka hallaka dorinar.