Sudan Ta Bayyana Takunkumin Amurka A Kanta Da Cewa Ya Saba Ka'ida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22108-sudan_ta_bayyana_takunkumin_amurka_a_kanta_da_cewa_ya_saba_ka'ida
Gwamnatin Sudan ta bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba mata na tsawon shekaru da cewa ya saba wa dukkanin ka'idoji na diflomasiyya da na kasa da kasa.
(last modified 2018-08-22T07:00:22+00:00 )
Jul 11, 2017 14:51 UTC
  • Sudan Ta Bayyana Takunkumin Amurka A Kanta Da Cewa Ya Saba Ka'ida

Gwamnatin Sudan ta bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba mata na tsawon shekaru da cewa ya saba wa dukkanin ka'idoji na diflomasiyya da na kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Gandur ya kirayi gwamnatin Amurka da ta cika alkawalinta na janye takunkuman da ta dora ma Sudan, domin kuwa sun saba wa dukaknin kai'idoji na diflomasiyya.

Wannan kira ya zo ne a daidai lokacin da ake sa ran Amurka za ta janye takumkuman da ta dora ma Sudan tun 1997, bayan da Sudan din ta mika wuya ga sharuddan da Amurka ta gindaya mata, tare da yin kamun kafa da gwamnatin Saudiyya domin samun rangwame daga gwamnatin Trump.