Halayyar Nuna Wariyar launin Fata Ta Shugaban Kasar Faransa.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22168-halayyar_nuna_wariyar_launin_fata_ta_shugaban_kasar_faransa.
Halayyar Nuna Wariyar launin Fata Ta Shugaban Kasar Faransa.
(last modified 2018-08-22T07:00:23+00:00 )
Jul 14, 2017 01:56 UTC
  • Halayyar Nuna Wariyar launin Fata Ta Shugaban Kasar Faransa.

Halayyar Nuna Wariyar launin Fata Ta Shugaban Kasar Faransa.

Shugaban kasar faransa ya bayyana halin da nahiyar Afirka ta ke ciki da cewa; Rauni ne wayewa" kuma daga kalubalen da su ke gaban nahiyar da akwai haihuwar barkatai da kowane iyali su ke yi. Don haka yawan al'ummar da nahiyar ta ke da shi, yana daga cikin abubuwan da su ke hana ta ci gaba.

Macron ya yi batunci ne ga nahiyar da a cikinta ne aka sami daya daga cikin wayewa ( civilization) mafi dadewa a duniya, kuma ta fuskar al'adu da ci gaba, tana da su tun dauri.

Wancan ci gaban dadadde wanda kuma ya kasance a tare da dimin arzikin da Allah ya huwacewa nahiyar, sune su ka sa kasashen turai 'yan mulkin mallaka da su ka hada da Faransa din shiga nahiyar domin yin wawaso sannan kuma da sauya yanin da Afirka ta kasance a ciki.

Abinda a yanzu Macron ya kira raunin wacewa da ci gaba, ya asamo asali ne daga barnar da 'yan mulkin mallaka su ka tafka a nahiyar.

'Yan mulkin mallaka ne su ka samar yake-yake a cikin nahiyar da kuma ruruta wutar kabilanci da fadan addini, da su ne ke hana nahiyar ci gaba. Dalilai na tarihi kwarara suna tabbatar da cewa  mulkin mallaka ya raba wasu kasashe da yankuna da karfi da matsayin da su ke da su, sannan ya jefa su cikin rikici na kabilanci.

Ga misali; A kasar Rwansa yan mulkin mallakar Belgium ne su ka kafa gwamnati bisa kabilanci saboda kawai su suji dadin dadde al'ummar kasar. Ita kuwa Belgium ta gina wancan tsarin ne bisa dacewarsa da ka'idoji na falsafar turai. A jikin katunan zama 'yan kasa ana tubuta cewa mutum dan hutu ne ko dan tutsi. Wannan ne ya share fagen afkuwar kisan kiyashin kabilancin da ya faru daga baya.

 

Fadace-fadace da su ke faruwa a cikin kasashen Afirka ta tsakiya da Sudan ta kudu tushensu yan mulkin mallaka.

Tun daga zamanin mulkin mallaka zuwa yanzu kasashen Afirka ba su zauna lafiya ba, domin daga lokaci zuwa lokaci sai fada ya tashi a wani wuri. Haka nan cin hanci da rasha da badakala da dukiyar al'umma, duk tushenu 'yan mulkin mallakar da su ka kafa da tsarin da basu da alaka da tarihi da al'adun al'ummar wannan nahiya.

Mafi yawancin Juyin mulki da aka rika yi a baya a cikin nahiyar yana da alaka da kasashen mulkin mallaka wadanda su ke sauya gwmanatin da ba ta yi musu biyayya a wasu lokutan. Faransa kuwa ba ta da bakin fada a wannan fage. Shi kuwa juyin mulkin duk lokacin da aka yi shi, yana maida hannun agogo baya ne a ci gaban kasa.

Amma kuma duk da haka, kwararru sun yi imani da cewa nahiyar Afirka za ta zama cibiyar duniya a nan gaba.  Hervé Bourges kwararre akan nahiyar Afirka ya rubuta littafi mai taken: "Kawayen Afirka" a cikin ya ambaci cewa duk da matsalar da ake gani a yanzu ta sauyin yanayi da kwararar 'yan gudun hijira, anna gaba nahiyar Afirka za ta zama mai matsayi na musamman a siyasar kasa da kasa. Kuma a hakikanin gaskiya ma a yanzu, ita ce zuciyar duniya.

Kuma a halin yanzu din kasashen da dama na nahiyar suna kan turbar  ci gaba da gina