Burundi: Mutane Sun Jikkata Sanadiyyar Fashewar Nakiya A Birnin Bujumbura
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22318-burundi_mutane_sun_jikkata_sanadiyyar_fashewar_nakiya_a_birnin_bujumbura
Rediyon Faransa na kasa da kasa ya bada labarin fashewar nakiya a birnin Bujumbura tare da jikkata mutane da dama.
(last modified 2018-08-22T07:00:24+00:00 )
Jul 17, 2017 07:20 UTC
  • Burundi: Mutane Sun Jikkata Sanadiyyar Fashewar Nakiya  A Birnin Bujumbura

Rediyon Faransa na kasa da kasa ya bada labarin fashewar nakiya a birnin Bujumbura tare da jikkata mutane da dama.

Rediyon Faransa na kasa da kasa ya bada labarin fashewar nakiya a birnin Bujumbura tare da jikkata mutane 10.

Sai dai rahoton ya ci gaba da cewa abu ne mai yiyuwa a kara samun karuwar wadanda su ka jikkatan. Sai dai kuma wadanda su ka kai harin tun sun gudu.

A cikin kwanakin bayan nan ana yawan kai hare-hare da nakiyoyi da a cikin fadin kasar.

Kasar ta Burundi dai ta fada cikin matsalar tsaro ne a 2015 da shugaban kasar Peer Nkurinziza ya yi tazarce.