Nijar : Mutane 23 Suka Mutu Sanadin Ambaliyar Ruwa
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD a Jamhuriya Nijar ya ce akalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu sanadin ruwan sama da ake ci gaba da tafkawa a wannan kasa dake yankin hamada sahara tun cikin watan Yuni.
A rahoton da ya fitar ofishin na OCHA ya ce zuwa ranar 10 ga watan Yuli nan kimanin mutane 19,500 ne, kwatamcin muhalai 2,405 ne ambaliyar ruwa saman sukayi wa barna, a yayin da adadin mutanen da suka riga mu gidan gaskia ya kai 23 a duk fadin kasar.
A jihar Tawa kuwa dake yammacin kasar ruwan sama sunyi awan gaba da dabbobi mayan da kananansu 4,000 a cewar rahoton.
Yamai babban birnin kasar na daga cikin yankinan da ambaliyar ta fi yin barna inda yara tara suka rasa rayukansu, bayan da gidaje suka rufta a kansu.
A jihar Agadas dake arewacin kasar ruwan sama da aka tafka a birnin da kewayensa sun awan gada da gada daya cilo data hada babbar hanyar zuwa garin Arlit mai arzikin karshen urenium lamarin da yawo cikas ga sifirin al'umma na 'yan kwanaki.
Ko baya ga hakan a yankuna da dama na kasar ambaliyar ruwan ta hadasa barna mai yawa da kuma awan gaba sa filayen noma masu yawa
Dama tun kafin hakan MDD ta yi kururuwa gameda barazanar ambaliyar ruwa a bana wacce zata iya shafar mutane sama da dubu dari da shida.