An Yankewa Mutane 28 Hukuncin Kisa A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22478-an_yankewa_mutane_28_hukuncin_kisa_a_masar
Kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira ta yanke wasu mutane 28 daga cikin mutane 67 da take zarkin da ayyukan ta'addanci a jihohin kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:26+00:00 )
Jul 22, 2017 14:44 UTC
  • An Yankewa Mutane 28 Hukuncin Kisa A Masar

Kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira ta yanke wasu mutane 28 daga cikin mutane 67 da take zarkin da ayyukan ta'addanci a jihohin kasar

Tashar Telbijin din Aljazera ta kasar Katar ta habarta cewa a wannan Assabar Kotun hukunta manyan laifuka ta kudancin birnin Alkahira bisa jagorancin mai shara'a Hasan Farid ta yankewa wasu Misrawa 28 hukuncin kisa bisa zarkinsu da hannu wajen kashe Hisham Barakat tsohon babban alkalin kasar.

Ko baya ga haka, babban alkalin na Masar ya zarkin Mutanan da kasancewa cikin kungiyoyin da ba su da rajista a cikin kasar, shiryar kisa da gagam, daukan makamai da ababen fashewa, karbar taimako daga kungiyoyin da aka kafa ba a kan ka'ida ba.

Rahoton ya ce sauran mutane 39 da ake zarki da kisan tsohon babban alkarin kasar an yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan Kaso.

A ranar 29 ga watan Yunin 2015, tsohon alkalin kasar ta Masar Hisham Barakat ya hallaka sanadiyar tashin Bam da aka dasa a Motarsa.