Sharhi:Ci Gaba Da Rikicin A Marocco
(last modified Wed, 26 Jul 2017 05:10:02 GMT )
Jul 26, 2017 05:10 UTC
  • Sharhi:Ci Gaba Da Rikicin A Marocco

A ci gaba da rikici gami da zanga-zangar nuna adawa da Gwamnatin kasar Marocco, mutane da dama ne suka shiga hannun jami'an tsaro a yankin Alhusaimah dake kudancin kasar

Duk da cewa yankuna da dama na kasar Marocco sun jima suna fuskantar zanga-zangar kin jinin Gwamnati, amma cikin makunin baya bayan nan, zanga-zanagar ta dauki wani sabon salo tun bayan da aka kame Naser Zafzafi shugaban matasa masu adawa da siyasar gwamnatin kasar, a halin da ake ciki, zanga-zangar kin jinin Gwamnati ta kara kamari a yankuna da dama na kasar, Zafzafi shi ne ya kafa kungiyar Alharaku-Sha'abi kuma shugaban masu adawa da rashin aikin yi gami bannar dukiyar Gwamnati a 'yan watanin nan, saidai a cikin kwanakin da suka gabata, hukumomi a kasar ta Marocco sun yi awan gaba da shi inda suke zarkinsa da tahar da hankali a cikin kasa kuma yanzu haka na tsare a gidan yari na garin Darul-Baida'a.

A zanga-zangar baya bayan nan da matasan garin Alhasimat suka yi , jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar, lamarin da yayi sanadiyar jikkatar mahalarta zanga-zangar da dama.

 A halin da ake ciki, Garin Alhusaimah dake arewacin kasar marocco ya zamanto wurin da ya fi daukan hankali Gwamnati, ganin yadda ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da siyasar ta.

A karshen watan Oktobar 2016, zanga-zangar aka yi a yankunan arewacin kasar ta samo asali ne  sanadiyar mutuwar Muhsin Fikri da ya kasance wani mai sayar da kirfi ne,hakan kuwa ya kasance ne a yayin da jami'an tsaro suka kwashe masa kifinsa sannan suka zuba cikin motar kwasar shara, inda nan take zuciyarsa ta buga ya fadi ya mutu.wannan lamari dai ya harziga al'ummar yankin inda tun daga wancan lokacin zuwa yanzu suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati tare da bayyana cewa Gwamnati ba ta kula da yankin su.

Saidai a nata bangare, Gwamnatin ta Marocco ta bayyana cewa yankin na Alhusaimah na son ballewa ne daga cikin kasar don haka ta daukin matakin amfani da karfi don masu zanga-zangar, a cewar Nau'am Chamsaki mai sharhi game da siyasar kasar ta Marocco, Gwamnatin Marocco na amfanin da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar nuna adawa da siyasar gwamnati,inda suka kame mutane da dama tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ci gaba da rikici gami da wanzuwar zanga-zangar kin jin Gwamnati zuwa wasu jihohin kasar ciki kuwa har da birnin Rabat fadar milkin kasar ya kara tayar da hankalin gwamnati.a halin da ake ciki, masu zanga-zangar na nuna adawar su kan yadda ake ci gaba da barnar dukiyar kasa, daga bangare wasu 'yan siyasa da masu rike da makamai gwamnati, gami da wasu kungiyoyin mafiya a kasar, inda suke bukatar sarkin kasar yayi garan bawul ga majalisarzartarwar kasar gami da Ma'aikatar tsaron kasar.

Kungiyoyin fararen hula na kasar sun bayyana cewa suna iya nasu kokari domin ganin an kawo karshen wannan zanga-zangar wacce ta samo asali daga zamanin farkawar Duniyar Larabawa da musulinci a shekarar 2011, kuma a ganin su, hanya guda da za ta kawo karshen wannan zanga-zanga ita ce daukan matakin yin garan bawul ga Gwamnati domin zagulo masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa, raba Dukiyar kasa cikin adalci gami da sallamar fursinonin siyasa a kasar.