Dauki Ba Dadi Tsakanin 'Yan Adawar Mauritaniya Da Jami'an Tsaron Kasar
Jami'an tsaron Mauritaniya sun farma taron 'yan adawar kasar da suka gudanar da taron gangami domin nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin kasar na gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a domin yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar.
Kakakin gamayyar 'yan adawar kasar Mauritaniya Salih Wuld Hanana ya sanar da cewa: Rundunar 'yan sandan Mauritaniya ta farma 'yan adawa da suka taru domin gudanar da taron gangami kan nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin kasar na gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan neman yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar, inda 'yan sanda suka dinga watsa iskar gas mai sanya hawaye tare da bugu da kulki lamarin da ya haifar da tarzoma.
Majiyar gwamnatin Mauritaniya ta sanar da cewa: Taron gangamin da 'yan adawar kasar suka kira a yankunan Assabahah da ke shiyar kudu maso yammacin birnin Nouakchott da kuma yankin Irfan da ke arewacin birnin, taruka ne da suka sabawa doka saboda babu izinin gudanar da su.
A ranar 5 ga watan Agustan wannan shekara ta 2017 ne ake sa-ran gudanar da zaben jin ra'ayin jama'ar Mauritaniya kan bukatar gwamnatin kasar na neman yin gyarar fuska a kundin tsarin mulkin kasar da ya hada da rusa Majalisar Dattijan Mauritaniya gami da canja tsarin tutar kasar.