An Kona Tutar Haramtacciyar Kasar Isra'ila A Masar
Wasu 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula sun gudanar da taron goyon bayan Masallacin Aksa a cibiyar kungiyar 'yan jaridun Masar tare da kone tutar HKI.
Hukumar gidan radio da telbijin na kasar Iran ta habarta cewa daga cikin mahaltar taron goyon bayan masallacin Aksa a birnin alkahirar na Masar har da Yahaya Alkazaz, da Rami Sha'as da suka kasance masu goyon bayan a haramta mu'amala da HKI, a yayin wannan taro, an bukaci Al'ummar musulmin Duniya da su haramta duk wani kaya da ya fito da HKI domin nuna adawa da ta'addancin da Sojojin HKI suke yi tare da nuna goyon bayan su da masallacin Aksa.
Muhamad Saeed Abdul-Hafiz manba a kwamitin majalisar kungiyar 'yan jarisu na kasar Masar ya yi kakkausar suka dangane da shurun da kasashen Larabawa suka yi game da ta'addancin jami'an tsaron HKI na baya bayan nan sannan kuma ya nemi uzuri ga Al'ummar Palastinu baki daya.
Daga ranar 14 zuwa 16 ga wannan wata na yuli da muke ciki ne jami'an tsaron HKI suka rufe kofofin Masallacin Al-Aksa,inda suka sanya na'urori na bincike ga masu salla, lamarin da ya janyo fishin Palastinawa