Zanga-Zangar Kin Jinin Shugaban Kasa A D/Congo
(last modified Tue, 01 Aug 2017 13:00:14 GMT )
Aug 01, 2017 13:00 UTC
  • Zanga-Zangar Kin Jinin Shugaban Kasa A D/Congo

Kungiyar Matasa mai fafutukar kawo sauyi a kasar Jumhoriyar D/Congo ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ta neman Shugaba Jaseph kabila ya sauka daga kan karagar milki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya litinin matasan Jumhoriyar D/Congo sun gudanar da zanga-zangar gama gari ta nuna adawa da ci gaba da zaman Shugaba Joseph Kabila a kan karagar milkin kasar, inda suka bukaci da a gudanar da zaben Shugaban kasar kafin karshen wannan shekara ta 2017 da muke ciki.

Ita dai wannan zanga-zanga ta samu goyon bayan daga kungiyoyin fararen hula da dama gami da jam'iyun siyasa na adawa a cikin kasar.

Rahoton ya ce rikici ya barke tsakanin mahalarta zanga-zangar da jami'an tsaro a birnin Goma cibiyar jihar Kivo ta arewa dake gabashin kasar, inda har jami'an tsaron suka yi awan gaba da mutane 10.

Har ila yau rahoton ya ce an cabke mutane 11 daga cikin mahalarta zanga-zangar a garin Butembo na jihar Kivo ta arewa.