Congo: Mutane 50 Sun Rasa Rayukansu A Wani Rikicin Kabilanci
Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar wani rikcin kabilanci a jamhuriyar Dimkradiyyar Congo, tare da jikkatar wasu da dama.
A wata zantawa da manema labarai da ya yi a yammacin jiya, shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na yankin Tanganyika a jamhuriyar dimukradiyyar Congo Tambana Nbami ya bayyana cewa, rikicin ya barke ne a tsakanin kabilun Pygmées Twa da kuma Bantous Lubas, inda mutane akalla 50 suka rasa rayukansu daga bangarorin biyu.
Rikici tsakanin wadannan mayan kabilu biyu ya fara ne tun a cikin watan Agustan shekara ta 2016 da ta gabata, an tura tawagar masu shiga tsakani a jiya domin tattaunawa da shugabannin kabilun biyu, da nufin samo hanyoyin sulhu da kuma kawo karshen zaman doya da manja da kabilun biyu suke yi a yankin.