An Kashe Ma'aikatan Red Cross A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta bayar da labarin kashe ma'aikatanta a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta Red Cross ta fitar a yau Laraba ta bayyana cewa, an kashe ma'aikatanta guda shida da suke gudanar da ayyukan jin kai da taimakon jama'a a wata cibiyar kiwon lafiya da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Bayanin ya ce hakika lamari ne mai matukar sosa rai, amma duk da haka kungiyar ba ta dakatar da ayyukan jin kai da take gudanarwa ga fararen hula na kasar ba.
Rikicin Afirka ta tsakiya dai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da tserewar fiye da wasu dubu 450 zuwa kasashen Chadi, Kamaru, da kuma jamhuriyar dimukradiyyar Congo.