Taho Mugama Tsakanin 'Yan Adawa Da 'Yan Sanda A Kasar Togo
(last modified Sun, 20 Aug 2017 06:21:22 GMT )
Aug 20, 2017 06:21 UTC
  • Taho Mugama Tsakanin 'Yan Adawa Da 'Yan Sanda A Kasar Togo

Jami'an 'yan kasar kasar Togo sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen duban masu zanga-zangar neman kawo karshen milkin iyalan gidan Gnassingbe

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya habarta cewa a jiya Assabar dubun masu adawa da gwamnatin kasar Togo sun gudanar da zanga-zangar kawo karshen gwamnatin iyalan gidan Gnassingbe da suka kwashe kimanin shekaru 50 suna milki a kasar, Shugaban kasar ta Togo mai ci Faure Gnassingbe ya hau kan karagar milkin kasar ne tun bayan mutuwar ma'aifinsa Gnassingbe Eyadema  a shekarar 2005 wanda ya kwashe kimanin shekaru 38 yana milki.

'yan adawar dake sanya da jajayen kaya, alamar babbar jam'iyar adawar kasar ta PNP sun bukaci gudanar da canji a kunmdin tsarin milkin kasar wanda zai kayyade wa'adin shugabanin kasar

Ko baya ga birnin Lome fadar milkin kasar, an gudanar da zanga-zangar  a wasu manyan buranen kasar inda rahotanni daga bangaren gwamnatin ke cewa  mutane biyu sun rasa rayukansu yayin  zanga-zangar a birnin Sokodé mai nisan kilomita 336 daga arewacin birnin Lome, bayan da wasu 25 suka jikkata daga cikin su akwai jami'an jandarma guda 12.

To saidai bangare 'yan adawar sun ce wadanda suka mutu sun kai mutane 7 kuma jami'an tsaro sun yi awan gaba da mahalarta zanga-zangar da dama.