An Bukaci Gwamnatin Nijer ta tattauna da 'yan adawa
Hadadiyar kungiyar ma'aikatan Nijer sun bukaci Gwamnati da ta tattaunawa da 'yan Adawa
A wata sanarwa da ta fitar jiya Assabar Hadadiyar kungiyar ma'aikatan Nijer wato ITN ta bukaci gwamnati da ta zauna kan tebirin shawara tare da 'yan adawar kasar domin warware takadamar da za ta hana su zuwa zabe, wanda hakan na iya janyo rashin amincewar zaben daga kungiyoyin kasa da kasa.
Kungiyar ta ITN ta bayyana damuwarta kan yadda bangaren 'yan adawar da Gwamnati suka yi gwaman jaki na kin zaman kan tebirin tattaunawa domin magance sabanin dake tsakaninsu.
A ranar 20 ga watan Maris ne za a gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu a jumhoriyar ta Nijer, inda shugaban kasa mai Alh mahamadou Issoufou zai fafata da shugaban 'yan adawa Malam Hama Amadou wanda ke tsare a gidan kaso na garin filingue kan zarkinsa da badagalar safafar jarirai, saidai 'yan adawar sun sanar da kauracewa zaben matukar ba a saki dan takararsu ba.