An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Togo
(last modified Thu, 07 Sep 2017 06:35:03 GMT )
Sep 07, 2017 06:35 UTC
  • An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Togo

Dubban jama'a ne suka fito kan tituna yayin wata zanga-zangar neman sauyi a birnin Lome na kasar Togo da kuma sauran wasu biranen kasar guda 10.

Darectan kungiyar kare hakin bil-adama ta Amnesty International reshen na Togo Aimé Adi  ya bayyana cewa adadin mutanen da suka fito zanga-zangar ya kai dubu 100 a birnin na Lome.

Daga nashi bangare madugun 'yan adawan kasar ta Togo Jean-Pierre Fabre cewa ya yi bai taba ganin irin wannan taro a birnin na Lome ba, inda dubban jama'a dauke da kwalaye ke ta furta kalaman nuna kyama ga shugaban kasar Faure Gnassingbé wanda yake rike da ragamar mulkin kasar tun daga shekara ta 2005.

Manyan jam'iyyun adawa na Togo akalla guda biyar ne suka kira wannan zanga-zangar, wanda a cewar madugun 'yan adawan ta samu karbuwa sabili da hadin kai na 'yan adawan.

Gwamnatin ta Togo dai ta soma bada kai bori ya hau, inda yayin wani taron majalisar ministocin kasar, ta sanar da wasu jerin sauye-sauye da za a aiwatar a kundin tsarin mulkin kasar ciki kuwa har da batun kayyade wa'adin mulki.