Shugaban Kasar Afrika Ta Tsakiya Ya Tsige Ministan Tsaron Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24005-shugaban_kasar_afrika_ta_tsakiya_ya_tsige_ministan_tsaron_kasar
Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya tsige ministan tsaron kasar daga kan mukaminsa.
(last modified 2018-11-18T09:03:40+00:00 )
Sep 13, 2017 12:24 UTC
  • Shugaban Kasar Afrika Ta Tsakiya Ya Tsige Ministan Tsaron Kasar

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya tsige ministan tsaron kasar daga kan mukaminsa.

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera a jiya Talata ya sanar da tsige ministan tsaron kasar Levy Yakete daga kan mukaminsa, kuma wannan mataki na shugaban kasar Afrika ta Tsakiya ya zo ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro suke ci gaba da habaka a kasar.

Tun a shekara ta 2014 kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da sunan Levy Yakete a cikin jerin sunayen mutanen da ake zargi da hannu a zubar da jinin bil-Adama a yakin basasar da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta tsunduma ciki tun a shekara ta 2013.