Jami'an Tsaron Masar Sun Kashe 'Yan Ta'adda 14 A Kasar
Jami'an tsaron Masar sun yi nasarar halaka wasu gungun 'yan ta'addan kasar akalla 14 a yankunan da suke shiyar arewacin kasar.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Masar Tamir Arrifa'i a yammacin jiya Laraba ya fitar da sanarwar cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun yi nufin kai harin wuce gona da iri kan wajen binciken ababan hawa a lardin Sina ta Arewa, amma kafin isarsu wajen jami'an tsaron Masar suka bude musu wuta lamarin da ya janyo halakar 'yan ta'adda shida da wasu jami'an tsaron kasar biyu.
Har ila yau a samamen da jami'an tsaron Masar suka gudanar a sassa daban daban na yankin Sina a jiya Laraba sun yi nasarar murkushe gungun 'yan ta'adda na mutane 8, yayin da gumurzu tsakanin bangarorin biyu ya jikkata jami'an tsaron kasar da dama.