Ambaliyar Ruwa Ta Lashe Rayukan Akalla Mutane 50 A Kasar Nijer
Sep 15, 2017 11:46 UTC
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Bullar matsalar ambaliyar ruwa sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a tsawon watanni uku ta lashe rayukan mutane akalla 50 a Jamhuriyar Nijer.
Ofishin Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya "OCHA" a birnin Yamai fadar mulkin Jamhuriyar Niger ya fitar da rahoton cewa: A tsawon watanni uku da suka gabata an samu bullar ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohin kasar Niger da ta janyo hasarar rayukan mutane akalla 50 tare da raba wasu kimanin 120,000 da muhallinsu.
Ambaliyar ruwar ta fi yin barna ce a babban birnin kasar Yamai sannan garuruwan Dosso, Tillaberi, Maradi da Zinder.
Tags