Fursunoni Sun Gudanar Da Yajin Cin Abinci A Gidan Kurkukun Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24181-fursunoni_sun_gudanar_da_yajin_cin_abinci_a_gidan_kurkukun_kasar_masar
Fursunonin siyasa a gidan kurkukun Al-Akrab da ke kudancin birnin Alkahira na kasar Masar sun gudanar da yajin cin abinci domin nuna rashin amincewarsu kan mummunar mu'amalar da suke fuskanta.
(last modified 2018-08-22T07:00:43+00:00 )
Sep 19, 2017 15:01 UTC
  • Fursunoni Sun Gudanar Da Yajin Cin Abinci A Gidan Kurkukun Kasar Masar

Fursunonin siyasa a gidan kurkukun Al-Akrab da ke kudancin birnin Alkahira na kasar Masar sun gudanar da yajin cin abinci domin nuna rashin amincewarsu kan mummunar mu'amalar da suke fuskanta.

A bayanin da kungiyar fursunonin siyasa da suke gidan kurkukun Al-Akrab na birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar ta koka kan irin mummunar mu'amalar da fursunonin siyasa suke fuskanta daga jami'an da suke kula da gidan kurkuku, don haka fursunonin suka dauki matakin gudanar da yajin cin abinci.

Kungiyar fursunonin ta fayyace cewa: Fursunonin siyasar suna fuskantar matsalar ganawa da iyalansu da suke son ziyartarsu a gidan kurkukun, kamar yadda mahukuntan gidan kurkukun ba su bari a kawo musu abinci da magunguna gami da kayayyakin bukatu da ake gabatarwa ga duk wani fursuna da ake tsare da shi a bisa al'ada.

Mafi yawan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin na kasar Masar ana tsare da su a gidan kurkukun Al-Akrab da ya yi kaurin suna a fagen cin zarafin bil-Adama a kasar, inda kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka sha fitar da rahotonnin cin zarafin bil-Adama a gidan kurkukun.