Togo: An Kashe Daya Daga Cikin Masu Zanga-zangar kin jinin Gwamnati
(last modified Thu, 21 Sep 2017 12:41:31 GMT )
Sep 21, 2017 12:41 UTC
  • Togo: An Kashe Daya Daga Cikin Masu Zanga-zangar kin jinin Gwamnati

Ofishin Shugaban Kasar Togo ya sanar da cewa harbin da aka yi a cikin masu Zanga-zangar ya yi sanadin mutuwar wani matashi dan shekaru 10.

Bugu da kari sanarwar ta ce baya ga karamin yaron da ya rasu, da kawai wasu mutane 25 da suka jikkata.

Sai dai ofishin shugaban kasar ya kore cewa jami'an tsaron kasar ne su ka yi harbin, tare da zargin cewa an kuma kai hari a gidajen manyan jami'an jam'iyyar da take mulkin a kasar.

Jam'iyyun hamayya sun dauke makwanni suna gudanar da Zanga-zanga akan manyan titunan biranen kasar suna masu yin kira ga shugaban kasar  Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma.