Sojojin Jumhuriyar Niger Sun Kashe Mayakan Boko Haram 4 A Jihar Diffa
Majiyar jami'an tsaro na jumhuriyar Niger ta bada labarin kashe mayakan boko haram 4 a jihar Diffa kusa da kan iyaka da tarayyar Nigeria a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto majiyar sojojin tana cewa tun cikin watan Yulin da ya gabata ne sojojin kasar suka fara wani farmaki na musamman don share jihar Diffa daga samuwar yayan kungiyar na ta Boko Haram.
Labarin ya kara da cewa sojojin sun kashe mayakan boko haram din ne a kauyen Corongul kusa da tabkin chadi sannan kan iyaka da tarayyar Nigeria, banda haka sun ganom makamai da kayakin aikin soje da dama a hannunsu.
A cikin shekaru ukku da suka gabata mayakan da Boko Haram sun zafafa hare hare kan mazauna yankin na Diffa musamman yankuna da ke makubtaka da tarayyar Nigeria , inda suka kashe mutane da dama wadanda suka hada da jami'an tsaro da kuma fararen hula.