'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Kin Jinin Shugaban Togo
Rahotanni daga kasar Togo sun bayyana cewar dubun dubatan masu adawa da ci gaban mulkin shugaba Faure Gnassingbe na kasar ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga duk kuwa da barazanar da jami'an tsaron kasar suka yi musu na daukar mataki a kansu.
Hadin gwuiwan jam'iyyun adawa na kasar Togon ne dai suka kira wannan zanga-zangar cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka kira al'umma da sauran magoya bayansu da su gudanar da zanga-zangar a ranakun yau Laraba da Alhamis suna masu zargin gwamnatin da kin amincewa da bukatar da suka gabatar cikin wasu jerin zanga-zangar da suka gudanar a kwanakin baya.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar wadanda suka fito cikin jajayen kaya sun taru a yankuna alal akalla guda uku a babban birnin kasar, kamar yadda jagororin adawan suka bukata, duk kuwa da barazanar amfani da karfi da ministan tsaron cikin gida na kasar yayi wa masu zanga-zangar.
Babbar bukatar 'yan adawan dai ita ce shugaban kasar Faure Gnassingbe ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan shekaru 12 yana mulki, suna masu kiran da a kawo karshen mulkin iyalan gidan Gnassingbe wadanda suka mulki kasar har na tsawon shekaru 50 bayan da mahaifin shugaban na yanzu Gnassingbe Eyadema ya mulki kasar har na tsawon shekaru 38.