'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutane Biyar A Yankin Sina' Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24986-'yan_ta'adda_sun_kashe_mutane_biyar_a_yankin_sina'_na_kasar_masar
Ma'akatar cikin gidan kasar Masar ta tabbatar da cewa wasu 'yan sanda uku da wani mai gadi bugu da kari kan wani farar hula guda sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addanci da wasu 'yan ta'adda suka lardin Sinai na kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:50+00:00 )
Oct 16, 2017 14:01 UTC
  • 'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutane Biyar A Yankin Sina' Na Kasar Masar

Ma'akatar cikin gidan kasar Masar ta tabbatar da cewa wasu 'yan sanda uku da wani mai gadi bugu da kari kan wani farar hula guda sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addanci da wasu 'yan ta'adda suka lardin Sinai na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar maharan sun kai hari ne da ababe masu fashewa da kuma bindigogi a wani wajen bincike na jami'an tsaro da suke gadin reshen babban bankin kasar Masar na garin Arish, babban birnin lardin na Sina'.

Hare-hare ga jami'an tsaro musamman a lardin na Sina' ya zamanto ruwan dare tun bayan juyin mulkin da sojojin kasar karkashin jagorancin shugaban kasar na yanzu Abdulfattah al-Sisi suka yi wa tsohon shugaban kasar Mohammad Morsi a shekara ta 2013.

Gwamnatin Masar din dai tana yaki da kungiyoyin ta'addanci da suke da alaka da kungiyar ISIS da suke ci gaba da kai hare-hare a lardin na Sina'i da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan jami'an tsaro a kasar.