Sudan Ta Maida Martani Kan Hana Amurkawa Zuwa Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25082-sudan_ta_maida_martani_kan_hana_amurkawa_zuwa_kasar
Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana irin halayen da gwamnatin Amurka take nunawa kasar masu karo da juna ne
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Oct 21, 2017 08:32 UTC
  • Sudan Ta Maida Martani Kan Hana Amurkawa Zuwa Kasar

Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana irin halayen da gwamnatin Amurka take nunawa kasar masu karo da juna ne

Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto ma'aikatar harkokin wajen kasar Sunan tana maida martani kan kiran da ministan harkokin wajen Amurka yayi na gargadiwa mutanen kasar kada su je kasar Sudan musamman yankunan Darfur da kuma Kurdufan.

Ma'aikatar ta kara da cewa gwamnatin kasar Amurka da kanta ta tabbatar da cewa an sami ci gaba a bangaren tsaro a kasar Sudan harma ta dage mata wasu takunkuman da ta dora mata, don haka akwai ban mamaki ta fidda sanarwan da ke hana Amurkawa zuwa sudan.

Rahoton ya kara da cewa gaskiaya ne an sami ci gaba a kasar sudan sannan banda haka gwamnati zata kare dukkan Amurkawan da zasu kawo ziyara a kasar Saudan.