Sudan Ta Zargi Amurka Da Halin Fuska Biyu
Oct 21, 2017 15:22 UTC
Sudan din ta soki Amurka ne saboda gargadin da ta yi yan kasarta dangane da zuwa kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya nakalto cewa; Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, a ciki ta kirayi 'yan kasarta da su kauracewa zuwa kasar sudan.
Sanarwar ta bakantawa shugabannin kasar Sudan da suke fatan dauke musu takunkumi da Amurkan ke shirin yi, zai kyautata alaka a tsakaninsu.
A lokacin shugabancin Barrack Obama,Kasar Amurkan ta rage wasu takunkumai da ta kakabawa Sudan, sai dai gwamnatin Donald Trump ta sake shigar da kasar a cikin jerin kasashe masu taimakawa ta'addanci.
Tags