Cutar Kwalara Ta Bulla A Yankin Yammacin Kasar Burundi
Mahukuntan Burundi sun sanar da bullar cutar kwalara a yankin da ke yammacin kasar, inda cutar ta fara lashe rayukan mutane.
Gwamnatin jihar Bubanza da ke yammacin kasar Burundi Tarsis New-Ngabu ya sanar da cewa: Tun bayan bullar cutar ta kwalara a jihar a tsawon makonni biyu da suka gabata ta lashe rayukan mutane akalla hudu, yayin da wasu kimanin 30 na daban suka kamu da cutar.
Jami'an kiwon lafiya a yankin jihar ta Bubanza sun bayyana cewa: Matsalar rashin tsabtaceccen ruwan sha ce ta janyo bullar cutar ta kwalara tare da jaddada bukatar aikewa da tallafin gaggawa da nufin ceto ran jama'a.
Kididdiga ta bayyana cewa: Mutane kimanin 3,140 ne suka kamu da cutar kwalara a watan Yuli zuwa Ogustan wannan shekara a lardunan kasar Burundi biyu, inda 117 suka rasa rayukansu kafin mahukuntan kasar suka samu nasarar shawo kan matsalar cutar.