Masar : An Yankewa Mutum 11 Hukuncin Kisa Kan Zargin Ta'addanci
Oct 23, 2017 07:51 UTC
Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu mutane 11 bisa zarginsu da alaka da wata kungiyar 'yan ta'adda.
Ko baya ga hakan kotun na zargin mutanen da yunkurin hallaka wasu mayan jami an tsaro biyu, kamar yadda wata majiyar shari'a ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.
Majiyar ta kuma ce kotun ta yi wa wasu mutane 14 daurin rai da rai a gidan kurkuku ciki har da wani samari dan shekara 10, koda ya ke kotun ta ce mutanen na da damar daukaka kara.
Ana dai zargin mutanen ne da alaka da wata kungiya mai tsatsarin ra'ayi a rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji sukayi wa hambararen shugaban kasar Mohamed Morsi a 2014.
Tags