An kori Daliban jami'ar Al-Azhar guda 4 a kasar Masar
An kori wasu daliban Jami'ar Al-Azhar guda 4 kan zarkin su da hanu wajen kisan tsohon babban Alkalin kasar A Masar
A wata sanarwa da ta fitar yau, Jami'ar Al-Azhar ta bayyana cewa ta kori wasu dalibanta saboda zarkin da ake yi musu da hanu wajen kisan tsohon Alkalin Alkalan kasar, rahoton ya ce an dauki wannan matakin ne bisa doka mai lamba 103 na kundin Jami'ar da hakan ke nuna cewa an kori wadannan dalibai guda hudu har abada daga Jami'ar.
Majiyar tsaron kasar ta ce ta gano 'yan ta'addar da suka hallaka Hisham Barakat tsohon babban alkalin kasar.
Kimanin watanni takwas kenan da aka sanya wani Bom a kalkashin motar Alkalin Alkalan kasar, inda bom din ya tashi da motar, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar Barkat, bayan an garzaya da shi asibiti, a can ne Alkalin alakan Hisham Barakat ya ce ga garin ku.