Oct 28, 2017 06:43 UTC
  • Hotunan Ran Gadin Ministan Harkokin Wajen Iran A Wasu Kasashen Afrika

Ministan harkokin waje na jamhuriya musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya dawo gida Tehran, bayan kammala wani ran gadinsa na kwanaki biyar a wasu kasashen Afrika.

A jamhuriya Nijar inda Mista Zarif, ya kammala ran gadin na sa, ya gana da mayan jami'an gwamnatin ta Nijar da suka hada da shugaba Mahamdu Isufu, da firayi minista Birji Rafini da kuma takwaransa na Nijar din Ibrahim Yacouba.

Kasashen biyu dai sun jaddada wajibcin yin hadin gwiwa don yaki da ta'addanci, bayan ga karkafa huldar dake tsakaninsu ta fuskar siyasa, kasuwanci, tattalin arziki da kuma makamashi.

Kafin Nijar dai Mista Zarif ya ziyarci kasar Uganda, inda ya jagoranci bikin bude wani katafaren asibiti na Iran a Kamfala babban birnin kasar ta Uganda.

A ziyara da ya fara daga Afrika ta Kudu a ranar Asabar data gabata, nan ma Zarif ya gana da mayan jami'an gwamnatin kasar a sahun gaba Shugaba Jacob Zuma.

Tags