An Dakatar Da Wasu Manya Manyan Jami'an Tsaron Kasar Masar Daga Aiki
An dakatar da wasu manya manyan jami'an tsaron kasar Masar daga aiki sanadiyyar hare-haren ta'addancin da suka auku a yankin Wahaad na lardin Giza.
Kamfanin dillancin labarann IRNA na kasar Iran ya nakalto Manja Janar Majdee Abdulqaffar ministan harkokin cikin gida na kasar yana fadar haka a jiya Asabar da yamma. Manja Janar Abdulgaffar ya kara da cewa wadanda abin ya shafa sun hada da Manja Janar Mahmood Shaarawi, wani kwamandan sojojin kasar, da Manja Janar Hisham Iraqi, mataimakin minista kuma shugaban ma'aikatar tsaro na Lardin Giza.
Har'ila yau ministan ya kara da cewa abin ya shafi Manja Janar Majdi Abul-khair shugaban dakarun tsaro na musamma, a ma'aikatar gudanarwa ta kasa.
Majiyar jaradar kasar Masar mai suna "Al-misriyyun " ta bayyana cewa sauke wadannan jami'an tsaro daga mukamansu yana da nasaba ne da hare-haren ta'addanci wadanda yan ta'adda suka kai a yankin Al-wahadd karkashin kula da lardin giza daga arewa maso gabacin kasar a ranar juma'ar da ta gabata, wanda kuma ya kai ga mutuwar jami'an tsaron kasar 16 da kuma fadawar makaman sojojin kasar a hannun yan ta'adda wadanda suka yi gaba da su bayan kisan jami'an tsaron.