Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Moroko
Al'umma a birnin Ribat fadar mulkin kasar Moroko sun gudanar da zanga-zangar cikan shekara guda da kisan gillar da aka yi wa wani mai sayar da kifi tare da jaddada yin kira kan sakin mutanen da aka kama domin nuna rashin amincewarsu da kisar.
Rahotonni sun bayyana cewa: Al'umma a birnin Ribat fadar mulkin kasar Moroko sun gudanar da zanga-zanga a jiya Asabar suna jaddada yin Allah wadai da kisan gillar da jami'an tsaron kasar suka yi wa wani mai sayar da kifi a garin Al-Hoceima tare da jaddada yin kira ga mahukuntan kasar kan sake duk mutanen da aka kama sakamakon zanga-zangar yin Allah wadai da kisan gillar.
Masu rajin kare hakkin bil-Adama da wakilan kungiyoyi har daga kasashen yammacin Turai sun fitar da bayanai suna jaddada bukatar sakin mutanen da aka kame kan zanga-zangar yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa mai sayar da kifin a shekarar da ta gabata.