Jami'an Tsaro 23 Ne Suka jikkata A Zanga-Zangar Yamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25255-jami'an_tsaro_23_ne_suka_jikkata_a_zanga_zangar_yamai
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce ‘yan sanda 23 ne suka jikkata a aragamar da suka yi da masu zanga-zangar adawa da daftarin dokar kasafin kudin kasar na shekara ta 2018 da aka yi ranar lahadi a birnin Yamai fadar mulkin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:30:55+00:00 )
Oct 31, 2017 06:43 UTC
  • Jami'an Tsaro 23 Ne Suka jikkata A Zanga-Zangar Yamai

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce ‘yan sanda 23 ne suka jikkata a aragamar da suka yi da masu zanga-zangar adawa da daftarin dokar kasafin kudin kasar na shekara ta 2018 da aka yi ranar lahadi a birnin Yamai fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labran kasar Faransa ya nakalto  ministan cikin gidan kasar Nijer Bazoum Mohamed, na cewa daga cikin jami'an tsaron 23 da suka jikkata 4  sun samu munanan raunuka, yayin da aka kona ko lalata motoci 14 cikin har da 10 na jami’an tsaro.

A lokacin tarzomar wadda kungiyoyin fararen hula suka kira, masu zanga-zangar sun kona ofishin ‘yan sanda da ke babbar kasuwar Yamai tare da farfasa wani bangare na ginin hukumar zaben kasar wato CENI.

Ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya zargin magoya bayan jam’iyyar adawa ta MODEN F/A Lumana wacce madugun'yan adawa Hama Amadou ke jagoranta da hannu waje da ke kokarin yin amfani da wannan dama domin shirya tarzama makamanciyar wadda aka yi a Burkina Faso domin kifar da gwamnati, sannan kuma ya zargi magoya bayan jam'iyar na kasashen wajen kamar Amurka da Turai da tunzura magoya bayan jam'iyar na kasa wajen tayar da tarzomar.

Ministan ya ce duk wanda aka sama da laifi a wannan tarzoma za a hukuntar da shi kamar yadda dokokin kasar suka shata.