Wani Madugun 'Yan Tawayen Kongo Ya Mika Kansa Ga Dakarun MDD
Rahotanni daga kasar Demokradiyyar Kongo sun bayyana cewar Kanar din sojin kasar da yayi tawaye da kuma daukar makami wajen yakar gwamnatin ya mika kansa ga dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD bayan wani gumurzu da magoya bayansa suka yi da dakarun kasar Kongon a yau din nan Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kakakin sojojin kasar Demokradiyyar Kongon Dieudonne Kasereka yana cewa gumurzun dai ya faru ne bayan da 'yan sanda suka yi kokarin kwance damarar Kanar Abbas Koyonga, wanda aka kora daga aikin sojin, sakamakon kin amincewa da hakan da shi da magoya bayansa suka yi.
Kakakin sojin ya ci gaba da cewa bayan barin wuta na wani lokaci Kanar Koyonga da wasu magoya bayansa sun mika kansu ga sansanin dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD da ke kasar Kongon, inda ya ce a yayin gumurzun dai akwai wasu da suka rasa rayukansu wasu kuma an samu an kama su sai dai bai yi karin bayani ba.
Kanar Kayonga din dai wanda a da ya kasance daga cikin daya daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen kasar Kongon wadanda aka shigo da shi cikin sojojin kasar bayan da aka kwance damarar tsohuwar kungiyar ta su, to sai dai kuma ya sake kaddamar da wani shirin tawayen ne bayan da aka kore shi daga aikin sojin a ranar Alhamis din da ta gabata.