Masar Ta Sake Zama Mamba A Kwamitin zartarwa Na UNESCO
An sake zabar kasar Masar a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar raya al'adu, ilmi da kimiyya ta MDD wato (UNESCO) a wani wa'adi na shekaru 4 masu zuwa.
An gudanar da zaben ne a lokacin babban taron UNESCO karo na 39 a birnin Paris.
Masar ta samu kuri'u 141 daga cikin 184 da aka kada a tsakanin kasashen Masar din da Iraq, da Jordan, da kuma Morocco.
Kasar Masar, da ma ta taba zama mamba a UNESCO daga shekarar 2013 zuwa 2017
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar ta bayyana cewa, Masar ta sake samun nasara a matsayin mamba a hukumar ta kasa da kasa ne sakamakon irin rawar da take takawa a harkokin diplomasiyya da kuma raya al'adu a mataki na kasa da kasa.
Masar ta yi amfani da damar domin yin godiya ga kasashe aminnanta kan goyan bayan da suka bata a wannan zaben, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Ahmed Abu Zeid ya sanar.