Masar: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda Masu Yawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25414-masar_sojoji_sun_kashe_'yan_ta'adda_masu_yawa
A wata sanarwa da sojojin na Masar suka fitar ta kunshi cewa; Sun kashe 'yan ta'addar da dama ne a harin da suka kai wa garin Sheikh Zuweid da ke arewacin Sinaa.
(last modified 2018-08-22T07:00:58+00:00 )
Nov 11, 2017 03:24 UTC
  • Masar: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda Masu Yawa

A wata sanarwa da sojojin na Masar suka fitar ta kunshi cewa; Sun kashe 'yan ta'addar da dama ne a harin da suka kai wa garin Sheikh Zuweid da ke arewacin Sinaa.

Bugu da kari, sojojin na Masar sun kame mutane 22 da ake zargi da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta "Ansaru Baitul Mukaddas."

Tun da fari a jiya juma'a wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'ya'yan kungiyar ce ta "Ansarul Baitul Mukaddas ne sun kashe direbobin manyan motoci 10 a yankin.

Yankin na Sinaa ya zama matattarar kungiyoyin 'yan ta'adda masu alaka da alka'ida da kuma Da'esh.

Masar ta yi asarar sojojinta masu yawan gaske a fadan da take yi da 'yan ta'addar da suke kai hare-hare a cikin kasar.