Shugaban Kasar Togo Ya Zargi 'Yan Adawan Kasar Da Tada Zaune Tsaye
(last modified Sat, 11 Nov 2017 11:06:08 GMT )
Nov 11, 2017 11:06 UTC
  • Shugaban Kasar Togo Ya Zargi 'Yan Adawan Kasar Da Tada Zaune Tsaye

Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbé, ya zargin masu adawa da gwamnatinsa da cewa suna kokarin tada da zaune tsaye a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Farasan ya bayyana cewar shugaba Faure Gnassingbé ya bayyana hakan ne a wani rangadi da ya kai wani barikin soji da ke kusa da birnin Lome, babban birnin kasar, inda yayin da ya ke tuhumar 'yan adawan kasar da neman tada da zaune tsaye ya bayyana cewar zanga-zangar da 'yan adawan suka gudanar a garuruwa daban-daban na kasar ya saba wa dokokin kasar lamarin da yayi sanadiyar tada fitina.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai 'yan adawa suka gudanar da wata zanga-zanga ta gama gari a garuruwa daban-dasban na kasar suna masu bukatar shugaba  Gnassingbén da ya sauka daga karagar mulkin kasar da kuma kawo karshe shekaru 50 na mulkin iyalansa a kasar.

'Yan adawan dai suna nuna adawa ne da kokarin shugaban Togon na yin tazarce a kan karagar mulkin kasar a zaben shekara ta 2020 da za a gudanar.