Jami'an Tsaron Sudan Sun Kama Madugun 'Yan Tawaye A Yankin Darfur
Sojojin kasar Sudan sun sanar da samun nasarar kama daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar na yankin Darfur a wani yanki na lardin Darfur din.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Sudan din SONA ya jiyo kakakin rundunar sojin Sudan din Birgediya Abdul Rahman Al-Ja'ali yana fadin cewa a yammacin jiya dakarun kasar sun sami nasarar kama Abdullah Rizig, daya daga cikin kwamandojin kungiyar 'yan tawayen nan ta Savana a arewacin yankin Darfur bayan wani gumurzu da ya gudana tsakanin sojojin gwamnatin da na 'yan tawayen.
Kakakin rundunar sojin da ake kira da Rapid Support Forces (RSF) ya kara da cewa tuni aka wuce da madugun 'yan tawayen zuwa birnin Khartoum don ci gaba da yi masa tambayoyi, yana mai cewa akwai yiyuwa a yi masa shari'a bisa laifin tawaye wa gwamnati wanda hukumcin hakan kisa ne. Kamar yadda har ila yau kuma ya ce a yayin gumurzun an kama wasu 'yan tawayen su 9 ciki kuwa har da wani daga Sudan ta Kudu.
Shi dai Abdullah Rizig ya kasance daga cikin dakarun sa kai na kan iyaka da suke aiki karkashin ikon sojojin Sudan din kafin daga baya ya zama dan tawaye bayan da gwamnatin Sudan din ta kuduri aniyar hada dakarun sa kai din cikin sojojin na RSF.