Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Togo
(last modified Mon, 20 Nov 2017 19:08:51 GMT )
Nov 20, 2017 19:08 UTC
  • Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Togo

Zanga-zangar kin jinin gwamnati ta dauki wani sabon salo a kasar Togo

Tajar talbijin aljazira ta habarta cewa a ranar lahadin da ta gabata dubun dubatan 'yan kasar ne suka gudanar da zanga-zangar neman shugaba Faure Gnassingbé ya sauka daga kan karagar milki a birnin Lome fadar milkin kasar, kafafen yada labaran gwamnati sun ce mahalarta zanga-zangar sun kai dubu 20, saidai 'yan adawa sun bayyana cewa mahalarta zanga-zangar sun haura mutane dubu 200.

Saidai duk da wannan kiraye kiraye da 'yan adawar kasar, shugaba Faure Gnassingbé ya dage a kan matsayinsa na dawwama kan kargar milkin kasar, sannan ya tuhumar 'yan adawan kasar da neman tada  zaune tsaye inda ya ce  zanga-zangar da 'yan adawan suka gudanarwa a garuruwa daban-daban na kasar ya saba wa dokokin kasar.

'Yan adawan dai suna nuna adawa ne da kokarin shugaban Togon na yin tazarce a kan karagar mulkin kasar a zaben shekara ta 2020 da za a gudanar, sannan kuma sun bukaci kawo karshen milkin shekaru 50 na iyalan gidan Gnassingbé.

hukumomin kasashen yammacin Afirka da manbobin kungiyar tarayyar Turai sun bunkaci bangarorin biyu da su zauna kan tebirin shawara, to amma 'yan adawa sun ce matukar dai ba a gudanar da canje-cenje a kundin tsarin milkin kasar ba, ba za su tattauna da gwamnati ba.