Masar : Harin Ta'addanci Ya Yi Ajalin Mutum 230 A Masallacin Juma'a
Wasu gungun 'yan ta'adda sun farma wani Masallacin Juma'a a lardin Sina ta Arewa da ke kasar Masar, inda suka kashe mutane fiye da 230 tare da jikkata wasu fiye da 100 na daban.
Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun farma wani Masallacin Juma'a a garin Arisha da ke lardin Sina ta Arewa na kasar Masar a lokacin sallar Juma'a a yau, inda suka bude wuta tare da tayar da bama-bamai a tsakanin masallata lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 235 tare da jikkata wasu giye da 100 na daban.
Har yanzu dai babu wata kungiya ko jama'a da suka dauki alhakin kai wannan mummunan harin ta'addanci amma dai ana nuna yatsar zargi kan kungiyar Ansaru-Baiti Maqdis da ta sanar da hadewarta da kungiyar ta'addanci ta Da'ish a shekara ta 2014, kuma wannan kungiyar ce ta yi kaurin suna a fagen kai hare-haren wuce gona da iri a lardin Sina ta Arewa.