Najeriya: An Gudanar Da Zanga-zangar Neman Sakin Sheikh Ibrahim El-zakzaky
Nov 25, 2017 18:55 UTC
Matan harkar musulunci sun yi Zanga-zangar ne a birnin Abuja suna masu neman a saki sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky da maidakinsa
Masu Zanga-zangar sun isa bakin ginin hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar dauke da hotunan Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky.
Tun a 2015 ne sojojin Najeriya suka kai hari a gidan Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky tare da kama shi da maidakinsa Malama Zinat.
Daruruwan mabiya Harkar musulunci a Najeriya ne dai aka kashe a yayin harin da sojojin suka kai, daga cikin hadda 'ya'yan sheikh, su uku.
Kotun kasar Najeriya ta bukaci da a saki Sheikh Zakzaky da mai dakinsa tare kuma da biyansu diyya.
Sai dai har yanzu gwamnatin kasar ba ta aiwatar da umarnin na kotu ba.
Tags