Ta'addanci : Masar Ta Dau Matakin Ba-Sani-Ba Sabo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25785-ta'addanci_masar_ta_dau_matakin_ba_sani_ba_sabo
Hukumomi a kasar Masar sun sanar da daukan matakan ba sani ba sabo akan yaki da ta'addanci.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 27, 2017 03:04 UTC
  • Ta'addanci : Masar Ta Dau Matakin Ba-Sani-Ba Sabo

Hukumomi a kasar Masar sun sanar da daukan matakan ba sani ba sabo akan yaki da ta'addanci.

Daga cikin matakan da hukumomin suka dauka har da kai hare-hare da jiragen sama kan sansanonin 'yan ta'adda da mabuyarsu da kuma hukuncin zama gidan yari mai tsari kan duk mahalukin da aka samu da laifin kai hari kan iyalan Misrawa.

Wannan matakin dai ya biyo bayan harin da wasu gungun 'yan ta'adda suka kai a ranar Juma'a data gabata wanda ya yi ajalin mutum sama da 300 ciki har da yara 27 a yankin arewacin Sinai.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai harin wanda shi ne irinsa mafi muni da kasar ta Masar ta gani a cikin 'yan shekarun baya baya nan, saidai masu bincike sun shaidawa ofishin mai gabatar da kara na gwamnatin Masar din cewa sun shaidu sun tabbatar masu da cewa maharan na dauke da tutar 'yan ta'addan IS.