Masar : Lauya Zai Sha Dauri Kan Kiran A Yi Wa Mata Fyade
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25971-masar_lauya_zai_sha_dauri_kan_kiran_a_yi_wa_mata_fyade
Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin zama gidan yari na shekara uku kan lauyan nan Nabih al-Wahsh, wanda ya kira a yi wa matan dake sanya wando ''jeans'' yagagge fyade.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Dec 03, 2017 02:22 UTC
  • Masar : Lauya Zai Sha Dauri Kan Kiran A Yi Wa Mata Fyade

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin zama gidan yari na shekara uku kan lauyan nan Nabih al-Wahsh, wanda ya kira a yi wa matan dake sanya wando ''jeans'' yagagge fyade.

Shi dai al-Wahsh, ya bayyana a wata muhawara talabijin a ranar 18 ga watan Oktoba da ya gabata cewa '' yi wa mata masu sanya matsatsan wando jeans yagagge fyade yiwa kasa hidima ne. 

An dai yanke wa Nabih al-Wahsh wannan hukuncin ne ba tare da ya halarci kotun ba.

Mista al-Wahsh dai na da damar daukaka kara.

Batun da lauyen na Masar ya yi dai ya janyo kace-nace ba kadan ba a kasar inda bangarori da dama suka shigar da kara a ofishin mi shigar da kara na gwamnatin kasar.

Kotun ta tuhumi al-Wahsh da firta kalamai dakan iya tada zaune tsaye a wannan kasa ta Masar inda wani binciken MDD na 2013 ya nuna cewa sama da kashi 99% na matan kasar sun taba fuskantar barazana ko dai ta cin zarafi ko neman taba jikinsu.