Nijar : An Kashe Wasu Jami'an Jandarma 3 da Soja Guda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2617-nijar_an_kashe_wasu_jami'an_jandarma_3_da_soja_guda
Hukumomi a jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar wasu jami'an tsaro kasar na Jandarma uku a garin Dolbel dake kan iyaka da Burkina Faso, yammacin kasar a yayin wani harin kwantar bauna da ake dangantawa dana kungiyar Al'Qaida reshen kasashen Larabawa wato AQMI ta kai masu a jiya Alhamis.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 18, 2016 07:10 UTC
  • Nijar : An Kashe Wasu Jami'an Jandarma 3 da Soja Guda

Hukumomi a jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar wasu jami'an tsaro kasar na Jandarma uku a garin Dolbel dake kan iyaka da Burkina Faso, yammacin kasar a yayin wani harin kwantar bauna da ake dangantawa dana kungiyar Al'Qaida reshen kasashen Larabawa wato AQMI ta kai masu a jiya Alhamis.

kazalika a cewar sanarwar wani sojan kasar guda ya rasa ransa kana wasu biyu suka raunana a wani harin kunar bakin wake da ake alakantawa dana Boko haram a garin Bosso mai iyaka da Najeriya a gabashin kasar, kamar yadda ministan cikin gida na kasar Hasoumi Masaoudu ya sanar.

wadanan hare-haren biyu na zuwa ne a kasa da kwanaki uku gabanin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za'a gudanar a ranar lahadin nan mai zuwa.