An Gudanar Da Zanga - Zangar Goyon Bayan Birnin Qudus A Kasar Tunisia
Masu zanga-zangar nuna goyon bayan Palasdinawa da kuma Birnin Qudus a matsayin mallakar Palasdinawa a jiya juma'a sun bayyana cewa duk wani kokarin maida huldar jakadanci tsakanin Tunisia da Haramtacciyar Kasar Isra'ila laifi ne ga mutanen kasar.
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin da suka shirya zanga-zangar a jiya a gaban majalisar dokokin kasar Kamal Al-gharbi yana cewa, sun shirya wannan zanga-zangar ce a dai-dai ranar da yahudawan Isra'ila suka kashe Mohammad Alzawayi dan asalin kasar Tunisia.
Masu zanga-zangar suna rera taken "Mutuwa ga Isra'ila" da kuma "Trump bai isa ya wulakanta al-uammar larabawa ba".
A ranar Laraba 5 ga watan Disamba da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da birnin Qudus a matsayin babban birnin gwamnatin HKI.