Faransa / Nijar : Hama Amadu Na Samun Sauki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2656-faransa_nijar_hama_amadu_na_samun_sauki
Dan takarar shugaban kasa a zagaye na biyu a Nijar Mal. Hama Amadu na samun sauki a jinyar da yake a Faransa, amma za'a ci gaba da duba lafiyar sa har tsawon kwanakii goma nan gaba, kamar likitan sa Luc Karsenty ya sanar.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 19, 2016 07:21 UTC
  • Faransa / Nijar : Hama Amadu Na Samun Sauki

Dan takarar shugaban kasa a zagaye na biyu a Nijar Mal. Hama Amadu na samun sauki a jinyar da yake a Faransa, amma za'a ci gaba da duba lafiyar sa har tsawon kwanakii goma nan gaba, kamar likitan sa Luc Karsenty ya sanar.

Dr Karsenty ya kara da cewa babu wata damuwa a yanzu game da lafiyar Hama Amadu.

A Ranar laraba da ta gabata ne aka garzaya da Hama Amadu a asibitin Amurka da ke kusa da birnin Paris domin sama masa da magani bayan tabarbarewar lafiyar sa a gidan kurkukun Filangue inda ake tsare da shi kusan watanni hudu.

kafin hakan dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta sanar da cewa ta yanke shawarar karbar Hama Amadu bisa dalilai ''na jin kai''