An Kashe Jami'an Tsaron Masar Biyu A Tsibirin Sinai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26629-an_kashe_jami'an_tsaron_masar_biyu_a_tsibirin_sinai
Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Masar biyu tare da jikkata wasu na daban a tsibirin Sinai dake arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:11+00:00 )
Dec 23, 2017 07:49 UTC
  • An Kashe Jami'an Tsaron Masar Biyu A Tsibirin Sinai

Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Masar biyu tare da jikkata wasu na daban a tsibirin Sinai dake arewacin kasar

A safiyar yau Asabar, wasu 'yan bindiga da suka yi kokarin kai harin ta'addanci sun fada cikin tarkon jami'an tsaro a tsibirin Sinai na arewacin kasar Masar, inda suka kashe 'yan bindigar uku tare da jikkata wasu hudu na daban,saidai a yayin fafatawar 'yan bindigar sun kashe jami'an tsaro biyu tare da jikkata wasu da dama na daban.

Yankin tsibirin sinai ta arewa ya zama maboyar kungiyoyin 'yan ta'adda musaman kungiyar ISIS wacce ta kaddamar da hare-hare a kan jami'an tsaro da al'ummar kasar Masar.

Kimanin shekaru uku kenan da kasar Masar ke fada da kungiyoyin 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar ISIS, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daruruwan jami'an 'yan sanda da sojojin kasar.