An Cimma Yarjejjeniyar Sulhu Tsakanin Congo Brazaville Da 'Yan Tawaye
Gwamnatin Kasar Congo Brazaville da 'yan tawayen yankin Pool sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa gwamnatin Congo Brazaville ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da 'yan tawayen yankin Pool wadanda suka fara tayar da kayar baya tun bayan zaben shugaban kasa na watan Afirilun 2016 .
Rikici tsakanin sassan biyu ya hana gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a mazabu da yawa kudancin kasar ta Congo.
'Yan tawayen da ake yi wa lakabi da 'ya'yan Pastor Ntumi sun yi alkawarin mika makamansu, yayin da gwamnati ta yi alkawarin shigar da su cikin rundunar sojojin kasar bayan sun kwance damarar yaki.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Congo da MDD, rikicin yankin ya janyo gudun hijra na fararen hular yankin kimanin dubu 263.